Nasarar Tinubu a kotu ta tabbatar da zabin ’yan Najeriya —Sanata Barau

Sanata Barau ya ce ’yan majalisa za su yi dokokin da za su taimaka wajen ganin Shugaba Tinubu ya cika alkawuransa na ciyar da Najeriya gaba

Nasarar Tinubu a kotu ta tabbatar da zabin ’yan Najeriya —Sanata Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa da ta tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da cewa Tinubu ne zabin ’yan Najeriya.

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a sanarwar taya murna ga Shugaba Tinubu, wadda mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashiru ya fitar.

Sanata Barau ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya baki daya da su hada hannu da shugaban domin ciyar da kasar gaba.

“Hukuncin kotun ya sake tabbatar da zabin ’yan Najeriya. Yanzu lokaci ne da ya kamata a ajiye bambancin siyasa a zo a hada hannu da Shugaba Tinubu wajen ciyar da kasar gaba,” in ji sanarwar.

Ya kara da cewa a bangarensu na ’yan majalisa za su yi duk mai yiwuwa wajen yin dokokin da za su taimaka wajen ganin Shugaba Tinubu ya cika alkawuransa na ciyar da Najeriya gaba.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos