NDLEA ta kama matashi da wiwi ta miliyan 10 a Kano
Hukumar ta ce ta jima tana bin diddigin matashin.
Hukumar NDLEA ta ce ta kama wani matashi mai suna Umar Adamu-Umar ɗauke da tabar wiwi mai nauyin kilo tara, wadda darajarta ta kai Naira miliyan 10 a Jihar Kano.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Asabar, ta ce ta cafke matashin mai shekara 27 ne a ranar 6 ga watan Agusta.
- Mutfwang ya aike wa majalisar dokokin Filato ƙarin kasafin kuɗin N74bn
- Sojoji sun hallaka ’yan fashi 7 a Katsina
Hukumar ta kama shi ne a kan hanyar Kano zuwa Zariya, yana shirin safarar ƙunshi 19 na tabar wiwi daga Legas zuwa Kano.
Mai magana da yawun hukumar, Sadiq Muhammad-Maigatari, ya ce matashin ya amsa cewa shi ne yake safarar wiwin.
Kuma ya ce tun kafin a kama shi hukumar ta kwana biyu tana bin diddigin.