NLC ta fara yajin aiki kwana 99 da janye tallafin mai
NLC ta fara yajin aiki kan janye tallafin mai bayan ta kaurace wa zaman sulhudn da Gwamnati ta kira
A yau Talata Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ke fara yajin aiki a fadin kasar, saboda tsadar rayuwar da al’umma suke fama da ita sakamakon janye tallafin mai da Gwamnatin Tarayya ta yi.
NLC ta fara yajin aiki gargadi na kwana biyu a fadin kasar ne washegarin da ta kaurace wa zaman sulhun da gwamnatin ta gayyace ta da nufin ganin kungiyar ta hakura.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin rufe kasuwannin dabbobi 8 a Zamfara
- Shugabannin ’yan kwadago sun kauracewa zama da Gwamnatin Tarayya
Yajin aikin na zuwa ne kwanaki 99 bayan Shugaba Bola Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanar da kawo karshen tallafin a yayin jawabinsa na fara aiki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.
Hakan ya haddasa ninkuwar farashin litar man daga N197 zuwa 620, wanda kuma ya yi sanadin hauhawar farashin kayan masarufi da na sufuri da sauran bangarorin rayuwa.
Tun a lokacin da Tinubu ya sanar da karshen tallafin kungiyar NLC ta yi watsi da matakin a matsayin riga-mallam-masallaci, bisa hujjar cewa gwamnati ba ta yi tanadin abubuwan da ya kamata na rage tasirin janye tallafin ba da farko.
Kwanaki 40 da suka gabata, a ranar 26 ga watan Yuni, kungiyar ta gudanar da zanga-zanga a fadin kasar, da nufin shiga yajin aiki bayan hakan.
A ranar ce shugabannin kungiyar suka kai wa Majalisar Dokoki ta Kasa korafinsu, inda wakilan majalisar suka yi musu alkawarin ganin bangaren zartarwa ya yi abin da ya dace kan lamarin.
Amma a yammacin ranar farkon zanga-zangar fadar shugaban kasa ta zauna da shugabannin kungiyar, suka jingine batun, da cewa za su ba wa gwamnatin lokaci ta yi abin da ya kamata.
Daga bisani kungiyar ta sanar a ranar Juma’a cewa za ta koma yakin aikin, inda gwamnati ta hannun ministan kwadago Simon Lalong ta nemi yi zama da su da domin ganin sun janye yajin aikin ama kungiyar ta kaurace wa zaman.