NSCDC ta yaye sabbin jami’an tsaro 80 a Gombe
An koyar da su dabarun yaƙi ba tare da makami ba, tattara bayanan sirri, ladabi da ƙa’idojin aiki, agajin gaggawa da kuma kashe gobara
Hukumar tsaron farin kaya ta Sibil Didens (NSCDC) Reshen Jihar Gombe ta yaye sabbin jami’an tsaro 80 daga kamfanonin tsaro masu lasisi guda 10 da ke aiki a jihar.
An gudanar da horon na makonni biyu ne a harabar Sakatariyar Gwamnatin Tarayya ta Gombe, domin inganta aikin tsaro da kuma tabbatar da bin doka da ƙa’idojin da ke jagorantar kamfanonin tsaro masu zaman kansu.
Da yake jawabi yayin taron, Kwamandan Hukumar NSCDSC a jihar, Jibrin Idris, ya bayyana cewa shirin wani muhimmin mataki ne na inganta ƙwarewa da haɗin gwiwa a fannin tsaro.
Ya ce wannan ba biki bane kawai illa wata alama ta ƙudirin hukumar na ɗaga darajar aikin tsaro a tsakanin kamfanoni masu zaman kansu, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da dukiyoyi.
- An ƙona mutum 3 da ransu kan kisan basarake a Filato
- An kashe Basarake, matarsa da mutum 3 a Benuwe
- Kotu ta ɗaure mai zambar kuɗi da takardun bogi
Kwamandan ya yaba wa jami’an bisa jajircewa da ladabinsu yayin horon, inda aka koyar da su dabarun tsaro daban-daban da suka haɗa da atisayen jiki, yaƙi ba tare da makami ba, tattara bayanan sirri, ladabi da ƙa’idojin aiki, agajin gaggawa da kuma kashe gobara.
Ya kuma buƙace su da su kasance jakadu nagari na tsaro a wuraren aikinsu, tare da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, ƙwarewa da riƙon amana.
Hakazalika, ya jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da gyara da inganta harkokin tsaro masu zaman kansu a jihar, tare da gargaɗin masu gudanar da ayyukan tsaro ba bisa ƙa’ida ba.
Manyan jami’an hukumar, wakilan kamfanonin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki sun halarci taron.