Ramadan: MDD ta bukaci al’ummar duniya su nuna tausayi da zaman lafiya

Ya yi kira ga kowa da kowa da ya yi amfani da wannan lokaci wajen karfafa hadin kai da kuma nuna kulawa ga masu fama da rashin zaman lafiya a sassan duniya

Ramadan: MDD ta bukaci al’ummar duniya su nuna tausayi da zaman lafiya

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres

Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada muhimmancin al’ummar duniya su rungumi zaman lafiya, tausayi da hadin kai a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara  azumin watan Ramadan.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya yi wannan kira ne a sakonsa na taya Musulmi murnar shigowar watan Ramadan na Shekarar 2026.

Mista Guterres ya ce watan Ramadan mai alfarma ba lokaci ne na ibada da tunani kawai ba, wata ne na karfafa bege da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Ya kuma yi kira ga kowa da kowa da ya yi amfani da wannan lokaci wajen karfafa hadin kai da kuma nuna kulawa ga masu fama da rashin zaman lafiya a kasashe daban-daban.

“Ga Musulmai a duk fadin duniya, watan Ramadan mai tsarki lokaci ne na tunani da addu’a. Yana kuma wakiltar zaman lafiya,” a cewar, Mista Guterres, yana mai nuna damuwa bisa rikice-rikicen da ke ci gaba da addabar al’umma a sassan duniya.

Ya bayyana cewa a kasashen Afghanistan, Yemen, Gaza, Sudan da wasu wurare, miliyoyin mutane na fuskantar “munanan tasirin rikici, yunwa, kaura, wariya da sauran matsaloli.

“A cikin wadannan lokuta masu wahala, mu saurari sakon da Ramadan ke dauke da shi wanda ba ya gushewa, don hada kan al’umma. Don kawo taimako da bege ga wadanda ke cikin wahala. Kuma don kare haƙƙoƙi da mutuncin kowane mutum.”

Mista Antonio Guterres wanda a duka shekara, yaka kai ziyara ta musamman ga al’ummar Musulmi masu azumi tomin yin ina buda baki da su, ya bayyana cewa, “kowace shekara nakan dawo da kwarin gwiwa daga ruhin Ramadan na zaman lafiya da tausayi.

“Allah Ya sa wannan wata Mai Tsarki ya zame mana abin da zai karfafa mu mu yi aiki tare a matsayin al’umma daya, domin gina duniya mai cike da zaman lafiya, karamci da adalci ga kowa da kowa.”