Ramadan: Jihar Sakkwato za ta kashe N1bn kan ciyarwar azumi
Gwamnatin ta kuma ƙara yawan cibiyoyin ciyarwar watan Ramadan da ke faɗin jihar daga 155 zuwa 170.
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta amince da kashe Naira biliyan ɗaya domin shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan na bana.
Gwamnatin ta kuma ƙara yawan cibiyoyin ciyarwa da ke faɗin jihar daga 155 zuwa 170.
Gwamna Ahmed Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ƙaddamar da kwamitocin da za su kula da ayyukan cibiyoyin ciyarwar a ranar Lahadi.
Ya ce ƙarin cibiyoyin ya biyo bayan korafe-korafe da kuma lura da matsalolin da aka samu a bara.
- Yau El-Rufai zai bayyana a ofishin EFCC
- NAJERIYA A YAU: Yadda Muka Yi Asarar Biliyoyin Naira A Kasuwar Singa Muna Ji Muna Gani
- Gobara: Barau ya bai wa ’yan kasuwar Singa tallafin N100m
A cewarsa, ana sa ran raba wa mutum 34,000 abinci a kullum a cibiyoyin ciyarwar tsawon watan Ramadan.
Ya ƙara da cewa kuɗin da aka ware, za a yi amfani da su ne wajen sayen kayan abinci, biyan ma’aikata da kuma sauran harkokin gudanarwa domin tabbatar da nasarar shirin.
Gwamna Aliyu ya yi kira ga masu hali da su rungumi al’adar taimaka wa marasa galihu, musamman a watan Ramadan da ke jaddada kyautatawa da tausayi.