Ranar Laraba za a soma dawo da Alhazan Katsina
Ana sa ran jirgin farko na Max Air zai taso daga Jeddah da misalin ƙarfe 1:00 na rana agogon Saudiyya a ranar Laraba.
Alhazai na dawowa daga Saudiyya
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Katsina ta sanar da cewa za a fara dawo da Alhazan jihar gida bayan kammala aikin Hajjin bana na 2026 daga gobe Laraba, idan Allah Ya kai mu.
A wata sanarwa da Kakakin Hukumar, Aliyu Haruna, tare da jami’in kula da jigilar Alhazai na kamfanin jirgin sama na Max Air, Alhaji Yusuf Ɗanbaba, suka tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho, sun ce an kammala shirye-shiryen fara jigilar Alhazan daga ƙasar Saudiyya zuwa Najeriya.
- Yadda kiwon kifi zai bunƙasa nahiyar Afirka — MDD
- An daure manomi shekara 15 kan laifin boye bayanan ayyukan Boko Haram
Sun bayyana cewa ana sa ran jirgin farko na Max Air zai taso daga Jeddah da misalin ƙarfe 1:00 na rana agogon Saudiyya a ranar Laraba.
Haka kuma, sun ƙara da cewa ana sa ran ƙarin jirage biyu za su ɗauko alhazan jihar a ranar Alhamis domin ci gaba da aikin dawo da su gida.
A cewarsu, gyare-gyaren da hukumomin Saudiyya suka riƙa yi kan jadawalin tashin jirage daga Jeddah ne suka janyo wasu sauye-sauye a lokutan jigilar mahajjatan.
Sai dai sun tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da dukkan shirye-shiryen cikin tsari domin tabbatar da an dawo da Alhazan Katsina cikin aminci da nasara.