Ruftawar kasa ta kashe mutum 30, an sace wasu 19 a Abuja
Mutum 30 sun mutu a sakamakon ruftawar kasa a wurin hakar ma’adinai, wasu mutum 19 kuma an yi garkuwa da su a Babban Birnin Tarayya Abuja
Mutum 30 sun mutu sakamakon ruftawar kasa a wurin hakar ma’adinai a Karamar Hukumar Kuje, ada ke karkashin Yankin Babban Birnin Tarayya.
Hakazalika, masu garkuwa da mutane sun sace mutum 19 a ranar Alhamis a Karamar Hukumar Bwari.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Bambanta Sheikh Giro Argungu Sauran Malamai
- Za a yi kiɗan ƙwarya da na shantu yayin auren zawarawa a Kano – Daurawa
Shugabannin kananan hukumomin shida na Yankin Babban Birnin Tarayyar ne suka sanar da Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, haka, a inda suka koka kan matsalar tsaro a kauyukansu.
“Babbar matsalarmu ita ce rashin tsaro a kananan hukumomin nan guda shida. Yau din nan aka yi garkuwa da mutum 19 a Karamar Hukumar Bwari. A karamar hukumata akwai mutum mutum biyar da yanzu kwanansu shida a hannun masu garkuwa da mutane,” in ji Ciyaman na Karamar Hukumar Kwali, Danladi Chiya.
Ciyamomin sun bayyana wa Wike cewa mutane 30 da suka rasu a ruftawar kasar, sun gamu da ajalinsu ne a yayin hakar ma’adanai da bisa ka’ida ba.
Shugaban Karama Hukumar Kuje, Abdullahi Sabo, ya zargi yadda gwamnati take ba da lasisin hakar ma’adinai barkatai da zama ummul-aba’isin yawaitar matsalar tsaro a yankunan.
“Barkatai ake ba da lasisin. Su ba an China, kwananan nan ruftawar kasa ta kashe mutum 30 a sakamakon hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba. Muna rokon ka (Wike) ka sa Ministan Ma’adinai ya hana wannan abu,” in ji shi.
A kan haka ne, Shugaban Karamar Hukumar Bwari, John Gabaya, ya yi kira da a rika aiki tare da shugabannin kananan hukumomi wajen rabon filaye a yankunansu.
Wike wanda ya bayyana dawuwarsa a game da hakan ya bukaci Daraktan hukumar saro a DSS da Kwamishinan an Sandan Abuja, su yi masa cikakken bayani kan garkuwa da mutanen, sannan su tabbatar da ceto wadanda aka sacen.
Ya umarci shugabannin kananan hukumomin su kafa kwamiocin sana ido kan sha’anin saro, sannan ya ce zai tattauna da Ministan Ma’adinai Dele Alake, domin kawo karshen ayyukan masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a birnin tarayyar.
Da yake magana a kan matsalolin da kananan hukumomin ke fuskanta, Ciyaman na Kwali, Danladi Chiya, ya bukaci Wike ya da Karamar Ministar Birnin Tarayya, Mariya Mahmoud, su magance matsalar karancin kudi da ke ci musu tuwo a kwarya.
“Ba ma samun isassun kudaden aiki, sannan ana ta raba wa bakin ido filayen yankunanmu, wanda idan aka ci gaba, karashenta, filayen makabartu da na wuraren ibadu ma za a iya bayarwa wasu; Abin da muke bukata shi ne a shigar da idan an tashi rabon filaye,” in ji shi.