Sabuwar Dokar BVN: Abubuwan da ya kamata ku sani

A ƙarƙashin sabon tsarin, masu asusun banki za su iya amfani da manhajar banki a waya guda ɗaya ce kacal

Sabuwar Dokar BVN: Abubuwan da ya kamata ku sani

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da sababbin dokoki kan tsarin amfani da lambar tantance masu ajiyar a banki (BVN).

CBN ya bayyana cewa waɗannan sababbin dokoki za su fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Mayu, 2026 domin ƙara tsaro a harkar banki da kuma rage zamba.

Sababbin dokokin za su shafi yadda ’yan Najeriya ke amfani da manhajojin banki da sauya wayar hannu da kuma gudanar da bayanan asusunsu.

Sababbin dokoki su ne:

Wayar hannu guda ɗaya kacal:

A ƙarƙashin sabon tsarin, masu asusun banki za su iya amfani da manhajar banki a waya guda ɗaya ce kacal. Idan suka canza sabuwar waya, za a cire da tsohuwar kai tsaye.

Haka kuma, duk wanda ya sauya waya dole ne ya bi ƙarin matakan tantancewa domin hana shiga ba tare da izini ba.

 

Ƙarin sa ido kan zamba:

Bankin CBN ya ce zai ƙara sanya ido kan duk asusun banki da ake zargi da aikata ba daidai ba.

Duk BVN da aka gano yana da wata alama ta zargi, za a sanya shi cikin bincike na sa’o’i 24, inda bankuna za su iya taƙaita ko dakatar da asusun.

 

Taƙaita canza lambar waya:

Sabon tsarin ya kuma tanadi cewa za a ba masu asusun banki damar canza lambar waya sau ɗaya kacal.

Wannan mataki na da nufin rage zamba ta hanyar sauya SIM (SIM-swap).

 

Sababbin ka’idojin rajista:

An kuma ƙara tsaurara sharuɗɗan yin rajista, inda sai mutum ya kai shekara 18 kafin ya mallaki BVN.

Ƙananan yara za su riƙa amfani da asusun banki ne ƙarƙashin kulawar iyaye ko masu kula da su.

 

Taƙaita tura kuɗi bayan canza waya:

Idan mutum ya canza waya, za a taƙaita masa tura kuɗi zuwa N20,000 na tsawon awa 24 kafin a dawo masa da cikakken iko.

CBN ya ce an ɗauki matakan ne domin ƙara tsaro a harkar banki.