Sahun farko na alhazan Kano sun sauka a Madina

Maniyyata 558 ne suka bi jirgin farkon da suka haɗa da maza 333 da mata 225 daga wasu ƙananan hukumomi huɗu.

Sahun farko na alhazan Kano sun sauka a Madina

Rukunin farko na maniyyatan Jihar Kano sun sauka a birnin Madina na ƙasar Saudiyya gabanin gudanar da aikin Hajjin bana.

A safiyar Asabar ɗin nan ne dai maniyyatan suka sauka a birnin da misalin ƙarfe 7.35 agogon Najeriya, bayan sun baro Kano da tsakar dare a jirgin kamfanin Max Air.

Maniyyata 558 ne suka bi jirgin farkon, inda suka haɗa da maza 333 da mata 225 daga wasu ƙananan hukumomi huɗu.

Ƙananan hukumomin sun haɗa da Dala da Fagge da Gwale da Ungoggo da kuma