Sama da masunta 3000 ne suka shiga gasar kamun kifi ta Argungu

Masunta sun shiga ruwa domin neman sa’arsu a cikin ruwan na Argungu.

Sama da masunta 3000 ne suka shiga gasar kamun kifi ta Argungu

Sama da masunta 3000 ne suka shiga gasar kamun kifi ta bana a garin Argungu, a gaban Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu.

Shugaban ƙasa ya isa wajen gasar kamun kifin na Matan Fada kamar yadda aka saba da misalin ƙarfe 2:32 na rana.

Sarkin Ruwa na Argungu ne ya sanar da fara gasar, inda ya bai wa masunta damar shiga ruwa domin neman sa’arsu.

Masunta sama da 3000 sun yi ta ƙoƙarin kamo manyan kifi domin samun nasarar lashe kyaututtuka da suka haɗa da mota da kuɗaɗe.

Shugaban ƙasa tare da gwamnoni daga jihohin Imo, Sakkwato, Zamfara, Jigawa, Gombe da Borno tare da Gwamnan Jihar Kebbi Nasir Idris suka halarta.

Sauran da suka halarci bikin kamun kifin na shekarar 2026, sun haɗa da ministoci da sarakunan gargajiya.