Samanja: Tauraron wasan kwaikwayo ya rasu yana da shekaru 84

Za a yi jana’izar fitaccen dan wasan kwaikiwayo Samanja Mazan Fama a safiyar yau Asabar a Kaduna bayan ya rasu yana da shekaru 84

Samanja: Tauraron wasan kwaikwayo ya rasu yana da shekaru 84

Marigayi Usman Baba Fategi ya yi fice a shahararren wasan kwaikwayo mai suna Zamanja Mazan Fama

Fitaccen dan wasan kwaikwayo, Usman Baba Fategi, wanda aka fi sani da Samanja ya riga mu gidan gaskiya.

Daya daga cikin mayan ’ya’yansa, Mohmmaed Usman, ya shaida wa Aminiya cewa Marigayi Samanja ya rasu ne a safiyar Asabar yana da shekaru 84, bayan fama da jinya yana.

Mohmmaed ya bayyana cewa mahaifin nasu ya rasu ne da misalin karfe 12 kuma za a yi jana’izarsa da misalin karfe 10 na safe a Masallacin Juma’a na unguwar Kabala Costain da ke Kaduna.

Mohamm Samanja, wanda tsohon soja ne, daga baya ya zama ma’aikacin Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, inda ya yi fice a shahararren wasan kwaikwayo mai suna Samanja Mazan Fama.

Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 12.

DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?

Cutar Anthrax ta ɓarke a Zamfara

Faston da ke yi wa ’yarsa fyaɗe tsawon shekaru ya shiga hannu

Trump ya rattaba hannu kan gomman dokokin zartarwa