Saudiyya ta rage tazarar kira da tayar da Sallah a lokutan Hajji

Ma’aikatar ta kuma bayar da umarnin taƙaita huɗubar Sallar Juma’a zuwa mintuna 15 har tayar da iƙama.

Saudiyya ta rage tazarar kira da tayar da Sallah a lokutan Hajji

Ma’aikatar Kula da Harkokin Musulunci ta Saudiyya ta bai wa Masallatan da ke birnin Makkah, umarnin rage tazarar da ke tsakanin kiran sallah da ta da iƙama a lokacin aikin Hajjin bana.

Dalilin wannan umarnin dai, tazarar kiran sallar asuba da ta da sallah ya koma minti 15, yayin da na sauran salloli ya koma minti biyar.

Ma’aikatar ta kuma bayar da umarnin taƙaita huɗubar Sallar Juma’a zuwa mintuna 15 har tayar da iƙama.

Ma’aikatar ta ce dalilin hakan shi ne domin sauƙaƙa kai-ka-kawo tsakanin mahajjata, saboda cinkoso.

Ana sa ran duk masallatan da ke kewayan masallatan Harami da kuma sauran wuraren aikin Hajji za su bi wannan umarnin.