An bindige mutane 5 a harin masallaci a Amurka

Mahara sun bude wuta a masallaci mafi girma yankin San Diego da ke California a kasar Amurka.

An bindige mutane 5 a harin masallaci a Amurka

Cibiyar Musulunci ta San Diego

Wasu matasa biyu dauke da bindigogi sun bude wuta a masallaci mafi girma a gundumar San Diego a Jihar California da ke kasar Amurka.

Rahotanni sun bayyana cewa mahran, sun harbe wani jami’in tsaron masallaci da wasu maza biyu har lahira a Cibiyar Musulunci ta San Diego a yayin harin na ranar Litinin.

Limamin masallacin kuma daraktan Cibiyar Musulunci, Taha Hassane, ya ce, “Ba mu taɓa fuskantar bala’i irin wannan ba a baya. Wannan abin takaici ne ƙwarai a kai hari kan wurin ibada.”

Daruruwan jami’an tsaro da aka kira zuwa wurin sun iske gawarwakin maza uku da ke da alaƙa da masallacin da aka harbe har lahira.

Jami’ai sun yaba da mai tsaron da aka kashe a matsayin wanda watakila ya taimaka wajen hana ƙarin zubar da jini.

Bayan ɗan lokaci, Hukumar ’yan sandan jihar ta ce ta gano gawarwakin maharan, masu shekaru 17 da 18, a cikin mota a tsakiyar titi, dukkansu da alamun sun harbi kansu da kansu.

Kwamishinan ’yan sandan San Diego, Scott Wahl, ya ce jami’an tsaro na cikin gida tare da Hukumar FBI suna binciken harin da aka kai kan masallaci mafi girma masallaci a gundumar San Diego a matsayin laifin kiyayya.

Sai dai babu wani dalili na musamman ko abin da ya tayar da rikicin harbin bindigar da hukumomi suka bayyana a fili.

Hukumomi sun bayyana cewa an kirga dukkan yaran da ke halartar makarantar rana a cikin ginin masallacin kuma suna lafiya bayan harin da aka kai da misalin ƙarfe 11:40 na safe.

Wahl ya bayyana cewa mahaifiyar ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi ta kira ’yan sanda kusan sa’o’i biyu kafin harbin don sanar da cewa ɗanta, wanda ta bayyana a matsayin mai son ya kashe kansa, ya gudu daga gida bayan ya ɗauke bindigoginta guda uku da motarta.

A cewar kwamishinan, mahaifiyar ta ce ɗanta yana tare da wani abokinsa kuma dukkansu sun sanya kayan yaƙi na sojoji.

’Yan sanda sun bi sawun matasan tare da aika jami’an sintiri zuwa wani babban kantin sayar da kaya da kuma makarantar sakandaren ɗan nata a matsayin matakin kariya. Ana cikin haka ne sai kira ya shigo yana ba da rahoton harbin a masallaci.

Kwamishinan ya ƙi bayyana abin da ke cikin wata takarda da ya ce mahaifiyar wanda ya gudu ta samu.

Hukumar FBI ta bayyana sunan maharan da Caleb Liam Vazquez mai shekara 18, da keuma Cain Lee Clark mai shekara 17, kuma dukkansu mazauna San Diego ne.

Hukumar ta ce da alamar sun hadu ne a intanet, amma daga baya suka hadu fuska da juna, kafin su kai harin, a cewa jami’in FBI  mai kula da shiyyar, Mark Remily.