Sauraron karar da Nafiu Bala ya shigar rashin ladabi ne —Kotu
Alkalin ya ce karar da ke gaban kotun koli na iya kawo karshen batun gaba daya, don haka ya zama dole a dakatar da ci gaba da shari’ar a kotun tarayya har sai kotun koli ta yanke hukunci
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dage shari’ar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar ADC, Nafiu Bala, ya shigar kan jagorancin David Mark a jam’iyyar.
A zaman kotun na ranar Talata, Mai Shari’a Emeka Nwite ya bayyana cewa “rashin ladabi na shari’a” ne a ci gaba da sauraron karar a matakin kotun tarayya alhali akwai daukaka kara da ke gaban kotun koli.
Ya kara da cewa karar da ke gaban kotun koli na iya kawo karshen batun gaba daya, don haka ya zama dole a dakatar da ci gaba da shari’ar a kotun tarayya har sai kotun koli ta yanke hukunci.
A cikin karar da aka shigar ranar 2 ga Satumba, 2025, Nafiu Bala ya lissafo jam’iyyar ADC, David Mark, Rauf Aregbesola (sakataren jam’iyya na kasa), Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), da Ralph Nwosu, wanda ya kafa jam’iyyar kuma tsohon shugaban jam’iyya, a matsayin wadanda ake tuhuma.
Nafiu Bala ya dage cewa bai taba yin murabus daga mukaminsa na mataimakin shugaban jam’iyya ba, don haka bisa tsarin jam’iyyar ya kamata shi ya karbi shugabanci bayan ficewar Nwosu. Daga bisani ya ayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, yana mai alkawarin kalubalantar jagorancin Mark a kotu.
A cikin karar, ya nemi kotu ta hana INEC amincewa da shugabancin David Mark, tare da tilasta hukumar ta dauke shi a matsayin shugaban rikon kwarya na ADC.
Haka kuma ya shigar da wasu bukatu na dakatar da jam’iyyar daga gudanar da tarurruka har sai an kammala shari’ar.
An fara sauraron bukatarsa ta gaggawa a ranar 4 ga Satumba, 2025, inda mai alkaci ya umurci wadanda ake tuhuma, ciki har da INEC, da su bayyana dalilin da zai hana a amince da bukatar Nafiu Bala.
A zaman kotun na baya-bayan nan, mai shari’a Emeka Nwite ya dage shari’ar ba tare da kayyade lokaci ba, yana mai cewa zai zama “rashin ladabi na shari’a” a ci gaba da sauraron karar a kotun tarayya alhali akwai daukaka kara da ke gaban kotun koli, wacce za ta iya kawo karshen batun gaba daya.
Kotun Koli ta ba da umarnin gaggauta sauraron karar ADC
David Mark, shugaban bangaren ADC da ke rikici da Nafiu Bala, ya daukaka kara kan hukuncin wucin gadi da Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta yanke.
Sai dai a ranar 12 ga Maris, 2026, Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da daukaka kararsa, tana mai cewa ba ta da tushe kuma ba ta da amfani.
Kotun ta umurci bangarorin da su koma kotun tarayya tare da ci gaba da kasancewa a matsayin da suke kafin rikicin har sai an yanke hukunci.
A ranar 1 ga Afrilu, Hukumar INEC ta sanar da cewa ba za ta kara hulda da bangaren ADC na Mark ko na Nafiu ba, bayan ta yi nazari kan hukuncin kotun daukaka kara. INEC ta ce za ta guji hulɗa da kowanne bangare, ciki har da sa ido kan tarurrukansu.
Bayan wannan mataki na INEC, bangaren Mark ya daukaka kara zuwa Kotun Koli, inda ya kalubalanci hukuncin kotun daukaka kara.
A ranar Talata, kwamitin alkalai biyar na Kotun Koli karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba ya amince da a saurari karar cikin gaggawa.