Sheikh Adam ya jagoranci limamai a Yobe wajen yi wa Najeriya addu’a
Duk wani ƙoƙarin ɗan adam, taimakon Allah shi ne mafi inganci wajen samun mafita a kowane yanayi.
Ƙungiyar limaman masallatai ta Najeriya, ƙarƙashin jagorancin shugabanta na ƙasa, Mohammad Nasiru Adam, ta gudanar da taro a Jihar Yobe domin yin addu’o’i na musamman ga ƙasar Nigeria da shugabanninta.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, mataimakin sakatare janar na ƙungiyar, Yusuf Abdullahi Yusuf, ya bayyana cewa ƙasar na fuskantar manyan ƙalubale biyu da suka haɗa da tsaro da kuma matsin tattalin arziki musamman a Arewacin Najeriya.
- Boko Haram ta kashe manoma da masu sana’ar itace 18 a Borno
- Walida: Kotu ta umarci DSS ta miƙa wa ’yan sanda jami’inta
A cewarsa, gudanar da irin wannan addu’a yana da matuƙar muhimmanci, inda ya jaddada cewa duk wani ƙoƙarin ɗan adam, taimakon Allah shi ne mafi inganci wajen samun mafita a kowane yanayi.
“Muna amfani da wannan dama wajen nutsuwa da yin tunani, tare da neman taimakon Allah ga ƙasarmu da muke ƙauna,” in ji shi.
A nasa jawabin, kwamishinan harkokin addini da sake fasalin ɗabi’a na jihar, Yusuf Umar, ya ce Najeriya ita ce kaɗai ƙasar da muke da ita, yana mai kira ga shugabanni da al’umma su ƙara dagewa da addu’a domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Shi ma babban limamin masallacin Yobe, Hudu Mohammad Yusuf, ya ce manufar taron shi ne wayar da kan jama’a kan muhimmancin addu’a, shiryar da shugabanni zuwa ga adalci, da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin limamai a faɗin ƙasar.
