’Yan Bindiga sun sace mutum 10, sun harbe 2 a Sakkwato

Bayan sace mutum 10 sun sace wasu mutane biyu.

’Yan Bindiga sun sace mutum 10, sun harbe 2 a Sakkwato

Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da mutane 10, ciki har da yara, sannan suka harbe wasu mutum biyu yayin wani hari da suka kai a ƙauyen Rimawa da daddare da ke Ƙaramar Hukumar Goronyo a Jihar Sakkwato.

Lamarin, a cewar mazauna ƙauyen, ya faru ne da misalin ƙarfe 12:55 na dare a ranar Alhamis, lokacin da maharan suka mamaye unguwar yayin da mutane ke barci a wajen gidajensu saboda tsananin zafi.

Wani mazaunin ƙauyen, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana wa manema labarai cewa ƙarar harbe-harbe ce ta tashe su daga barci.

“Muna barci a waje saboda zafi lokacin da suka zo. Ba zato ba tsammani muka ji ƙarar harbin bindiga muka kuma ga walƙiyar wuta a jikin bishiyoyi, ba mu sani ba ashe harbin bindiga ne. Da sauri muka boya yayin da suka fara dukan kofofin wasu gidajen da ke kusa da mu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, jami’an sa-kai (vigilantes) da jami’an tsaro sun isa wurin da misalin ƙarfe 1:20 na dare, lokacin da maharan suka fara janye jikinsu.

“Lokacin da suka zo, harbin ya ragu. Muna jin kukan mata ne kawai a wata unguwa da ke kusa mai suna Munlela,” in ji shi.

Majiyoyi sun bayyana cewa tun farko ’yan bindigar sun yi garkuwa da mutane 21 ne, amma daga baya suka saki wasu daga cikinsu.

“Sun saki mata biyu da jarirai uku, inda suka ce sace jarirai ba ya cikin tsarinsu na wannan harin,” in ji wata majiya.