Sojin Nijar za su iya mika mulki cikin watanni 9 —Tinubu

Tinubu ya ce juyin mulkin da aka yi a Nijar shi ya bude kofar wanda ya faru a kasar Gabon.

Sojin Nijar za su iya mika mulki cikin watanni 9 —Tinubu

Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce idan sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suna da gaskiya, a cikin watanni 9 suna iya shirya zaben da za a mayar da mulki ga gwamnatin farar hula kamar yadda aka yi lokacin mulkin Janar Abdusalami Abubakar a Najeriya bayan mutuwar Sani Abacha.

Tinubu wanda yake jawabi lokacin da ya karbi tawagar shugabannin Musulmin Najeriya a karkashin jagorancin Sarkin Musulmi, Muhammad Saad Abubakar, ya ce juyin mulkin da aka yi a Nijar shi ya bude kofar wanda ya faru a kasar Gabon.

Shugaban ya ce a matsayin Najeriya na makociyar Nijar, ba za ta taba barin dangantakarsu ta katse ba, yayin da yake cewa babu wanda yake bukatar zuwa yaki saboda ganin irin illar da yakin ya haifar a kasashen Ukraine da Sudan, amma kuma ya zama wajibi a dauki mataki mai karfi domin kauce wa illar da matakin zai haifar.

Tinubu ya ce lokacin da Abdusalami ke jagorancin Najeriya a cikin watanni 9 ya shirya zaben da aka kafa wannan dimokiradiyar a shekarar 1998 wadda ta samu nasara, saboda haka babu dalilin da zai sa sojojin Nijar ba za su yi haka ba.

Shugaban ya roki Sarkin Musulmi cewar ya zama wajibi ya koma Nijar domin sake ganawa da sojojin da suka yi juyin mulkin, saboda abin da suka yi ya saba ka’ida, inda ya kara da cewar da zaran sun yi abin da ya dace, za su janye takunkumin karya tattalin arzikin da ke wahalar da talakawan kasar.

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra