Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa

Ayyukan sun haifar da gagarumar nasara ga rundunar, inda muka hallaka mayaƙan, kuma muka ƙwato makamai da kayan yaƙi daban-daban.

Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 17 a Borno da Adamawa

Dakarun sojin Nijeriya sun hallaka aƙalla ’yan ta’adda 17 na Boko Haram a wasu hare-haren kwantan bauna da suka kai a jihohin Borno da Adamawa a tsakanin ranakun 23 ga Yuli zuwa 2 ga Agustan 2025.

Kyaftin Reuben Kovangiya, Daraktan Yaɗa Labarai na Rundunar Sojin Kasa ta Nijeriya, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya bayyana cewa sojojin ƙarƙashin rundunar Operation Hadin Kai sun kai hare-haren ne a ƙananan hukumomin Bama, Konduga, Gwoza, Magumeri, da Biu a Jihar Borno, da kuma Michika da ke Jihar Adamawa.

A cewarsa, an kuma gano ababen fashewa 14 da ’yan ta’addan suka dasa a wurare daban-daban wadanda dakarun suka samu nasarar tarwatsa su.

“Ayyukan sun haifar da gagarumar nasara ga rundunar, inda muka hallaka mayaƙan, kuma muka ƙwato makamai da kayan yaƙi daban-daban da suke amfani da su wajen kai hare-hare,” in ji Kyaftin Kovangiya.

Kyaftin Kovangiya ya ce wannan nasara na zuwa ne bayan bincike da leƙen asiri da aka gudanar tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro da sauran hukumomin ƙasa.

Ko da yake ana samun ci gaba a fagen yaki da ta’addanci a Arewa maso Gabas, amma har yanzu matsalar tsaro na ci gaba da addabar sassan ƙasar, musamman a jihohin Zamfara, Katsina da wasu yankunan Borno, inda mayaƙan Boko Haram ke ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula da dakarun.

Rahotanni sun nuna cewa, hare-haren ‘yan ta’adda na haifar da ƙalubale ga abinci da zaman lafiyar jama’a, musamman ga manoma da ke fuskantar barazanar kisa ko biyan haraji kafin su iya zuwa gonakinsu.

A wasu yankunan, ’yan bindiga na tilasta wa mutane biyan kuɗin kafin su shiga gona, lamarin da ke hana dubun dubatar fararen hula gudanar da harkokin noma, wanda hakan na ƙara tsananta matsin tattalin arziki da yunwa a yankunan.