Sojoji sun kashe manyan jagororin ’yan ta’adda a Katsina

Kashe su ya kawo babban cikas ga kasurgumin shugaban ’yan ta’adda, Muhammadu Fulani, wanda ake danganta da hare-haren ta’addanci a yankunan Matazu, Musawa, Charanchi da Kankia

Sojoji sun kashe manyan jagororin ’yan ta’adda a Katsina

Sojoji sun aika wasu manyan jagorin ’yan bindiga lahira a Jihar Katsina baya da suka yi wa ’yan ta’addan ruwan albarusai.

Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana nasarar da jami’an tsaro suka samu a fafutukar da ake yi kan ’yan ta’adda, bayan da sojoji suka hallaka manyan kwamandojin ’yan ta’adda hudu a yayin sintirin yaki a kan hanyar Turare zuwa Yantumaki.

A safiyar Juma’a ne ’yan ta’adda suka gamu da ajalinsu bayan da suka kai wa sojojin hari.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ta ce sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa, suka fatattake su, suka kuma hallaka duka hudu ba tare da an samu asarar rai daga bangaren sojojin ba.

An kwato bindiga kirar AK-47 mai cike da harsasai biyar, babura guda biyu, wayoyin hannu da kuma tsabar kudi Naira N153,400 a hannunsu.

Tabbayyana cewa wasu daga cikin wayoyin da aka kwato na dauke da hotunan mutanen cikin kayan sojoji, kuma an mika su don bincike.

Binciken farko ya gano sunayen wadanda aka hallaka da suka hada da Bishir Holami, Jamilu Baki, Ibrahim Doro, da Abdurraman Maje.

Gwamnati ta bayyana su a matsayin manyan kwamandoji da ke da hannu a hare-haren da suka addabi al’ummomin Gobirawa, Raddawa, Kuki da sauran kauyuka a Dutsinma da Matazu.

Gwamnatin ta bayyana kashe su a matsayin babban cikas ga shahararren shugaban ’yan ta’adda, Muhammadu Fulani, wanda ake danganta da hare-haren ta’addanci a yankunan Matazu, Musawa, Charanchi da Kankia.