Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 10, sun ceto wasu a Filato

Wannan nasara ta biyo bayan musayar wuta da aka yi kwanan nan tsakanin ’yan ta’adda da sojoji, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu sojoji da ’yan banga a yankin Wanka da ke gundumar Keram a ƙaramar hukumar Kanam ta jihar.

Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 10, sun ceto wasu a Filato

Dakarun sojoji na rundunar “Operation Enduring Peace” sun yi nasarar kashe ’yan ta’adda 10 tare da ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su, yayin wani samamen share fage da ya lalata sansanonin masu aikata laifuka a dajin Daji Madam, da ke tsakanin ƙauyukan Daba da Seri a Jihar Filato.

Wannan nasara ta biyo bayan musayar wuta da aka yi kwanan nan tsakanin ’yan ta’adda da sojoji, wanda ya yi sanadiyar mutuwar wasu sojoji da ’yan banga a yankin Wanka da ke gundumar Keram a ƙaramar hukumar Kanam ta jihar.

A wani farmaki na haɗin gwiwa da aka kai a safiyar Alhamis, dakarun sun nufi maboyar masu laifi da aka gano a Dogo Ruwa da Bogwas da ke cikin dajin.

Wannan ya kai ga kashe ’yan fashi 10 tare da ƙwato bindigogi, harsasai da sauran kayan aikata ɓarna na ’yan fashin.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh ya bayyana samamen a matsayin nasara don daƙile harin ’yan ta’addan.”

Kyaftin Oteh ya bayyana cewa samamen, wanda aka gudanar tare da haɗin gwiwar ’yan banga na yankin, ya yi nasarar ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su.

“Wannan samame, wanda aka gudanar a matsayin ɓangare na ci gaba da farmakin share fage mai taken Operation WUTAN DAJI, yana nuna jajircewar sojoji wajen maido da tsaro a hanyoyin da ’yan ta’adda ke bi.

“Sakamakon haka, da misalin ƙarfe 08:30 na safe, ranar 9 ga watan Afrilu, 2026, dakarunmu sun kafa shingayen dabarun yaƙi tsakanin Dutsen Zaki da dajin Odare. Yayin samamen, an hango gungun ’yan ta’adda a kan babura suna tafiya ta wata sananniyar hanya, kuma nan take dakarunmu suka afka musu tare buɗe masu wuta,” in ji kakakin.

A cewar rundunar, duk da tirjiya daga ɓangaren ’yan ta’addan, dakarun sun yi musu nisa, wanda ya kai ga “kashe ’yan ta’adda 10 yayin da wasu suka tsere cikin daji a guje, suna barin gawarwakin sauran a baya.”