Sojoji sun sake ceto wata ’yar Chibok a Borno
An ceto ‘yan matan Chibok 16 a bana.
Dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) da ke Jihar Borno a Arewa maso Gabashin Najeriya, sun ceto wata ‘yar makarantar Chibok, Mary Nkeki bayan shekara tara da sace ta.
Kamar yadda rahoton ya nuna, wannan daliba da aka ceto, na daga cikin ‘yan matan makarantar Chibok 276 da mayakan Boko Haram suka sace a ranar 14 ga Afrilu, 2014 a garin Chibok.
- Malaman addini sun shirya wa matasa bitar zaman lafiya a Yobe
- Nijar: ECOWAS ta yi watsi da gwamnatin rikon kwaryar shekara 3
An bayyana hakan ne ta bakin kwamandan rundunar OPHK, Manjo-Janar Gold Chibuisi, yayin da yake mika Mary Nkeki ga Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Borno, Zuwaira Gambo a barikin soja na Maimalari da ke Maiduguri.
A cewarsa, an ceto Mary, mai shekaru 27, a ranar 14 ga watan Agusta, 2023, daga hannun sojojin bataliya ta 81 na sojojin Najeriya da ke garin Dikwa mai iyaka da kasar Kamaru.
Ya kuma bayyana cewa sunan Mary (Maryam) yana lamba ta 55 daga cikin jerin sunayen ’yan matan makarantar Chibok da aka sace a watan Afrilun 2014.
Game da yadda aka kubutar da ita, Kwamandan ya ce: “Sojojin mu ne suka ceto Maryam, yayin da Adamu, mijinta ya mika wuya ga sojoji a makon da ya gabata a yankunan kan iyakar Kamaru.”
Ya ce zuwa yanzu, sun ceto ’yan matan sakandaren Chibok 16 tun farkon wannan shekara ta 2023 zuwa yanzu.
A cewar Maryam, ta haifi yara biyu tare da mijinta, amma sun mutu sakamakon rashin abinci mai gina jiki a dajin Gulumba na Karamar Hukumar Bama.
Ta bayyana cewa duk da ceton da aka yi mata, tana so ta sake haduwa da mijinta.
“Mijina yana raye kuma ina son shi har yanzu. Ban san ko yana Dikwa har yanzu ba ko kuma an dawo da shi Maiduguri, amma zan so mu sake haduwa idan haka zai yiwu,” in ji ta.