Sojoji sun tarwatsa sansanonin Boko Haram a Borno

A lokacin samamen, an tabbatar da cewa, ’yan ta’adda sun tsere daga ƙauyen Forfor bayan sun gano sojojin na ci gaba da fuskantar su.

Sojoji sun tarwatsa sansanonin Boko Haram a Borno

Sojojin rundunar haɗin gwiwa ta Arewa maso gabas, Operation Haɗin Kai, sun ci gaba da kai samame a Timbuktu Triangle, wanda ya tilasta wa ’yan ta’adda tserewa daga sansanonin da dama a Jihar Borno.

Majiyoyi sun ce ayyukan da suka shafe mako guda suna yi wanda ya fara a ranar Talata a ƙarƙashin Operation Desert Sanity wani ɓangare ne na samame da ake ci gaba da kai wa Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas.

A cewar majiyoyin, rukunin farko na yaƙin, wanda ya ƙunshi sojoji na birget ta 25, sassan na 28 Task Force Briged da kuma membobin CJTF sun ci gaba da tafiya a yankin Azir-Hawan Burum-Multe-Forfor, suna share hanyoyin da matsugunan ’yan ta’addan da ke kewaye da yankin.

A lokacin samamen, an tabbatar da cewa, ’yan ta’adda sun tsere daga ƙauyen Forfor bayan sun gano sojojin na ci gaba da fuskantar su.

Sojojin sun ce, ayyukan sun kasance wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na hana ’yan ta’adda ’yancin walwala, wargaza yankuna da kuma inganta ikon tsaro a faɗin Timbuktu Triangle da maƙwabta yankuna.

A cewar majiyoyin ana ci gaba da sa ido da kuma ci gaba da keɓe jama’a daga fuskantar ayyukan cin zarafi don bin diddigin ’yan ta’adda da ke tserewa don hana su sake taruwa wuri guda.