Super Eagles ta ƙi gayyatar Ahmed Musa wasa da Sao Tome

A cikin waɗanda aka gayyata dai akwai William Ekong da Tyronne Ebuehi da Semi Ajayi da kuma Wilfred Ndidi.

Super Eagles ta ƙi gayyatar Ahmed Musa wasa da Sao Tome

Ahmed Musa

Tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya ta Super Eagles, ta ƙi gayyatar kyaftin dinta, Ahmed Musa wasan neman shiga Gasar Kofin Afirka da za ta fafata da Sao Tome.

Bayanai sun ce, kociyan tawagar, Jose Santos Peseiro ne bai gayyaci Ahmed Musa ba zuwa wasan da za barje gumi ranar Lahadi 10 ga watan Satumba.

Najeriya ce za ta karɓi baƙuncin Sao Tome a wasan rukunin farko da za su fafata a Uyo, inda a wasan farko da Super Eagles ta ziyarci Sao Tome, ta ci ƙwallo 10-0.

A cikin waɗanda aka gayyata dai akwai William Ekong da Tyronne Ebuehi da Semi Ajayi da kuma Wilfred Ndidi.

Sauran sun haɗar da Frank Onyeka da Moses Simon, da Victor Osimhen da kuma Taiwo Awoniyi.

Haka kuma Peseiro ya gayyaci masu tsaron raga uku da suka haɗa da mai taka leda a gida Olorunleke Ojo da ‘yan wasan baya takwas da masu buga tsakiya huɗu da masu zura kwallaye a raga su takwas.

A karon farko an gayyaci Peseiro Jordan Torunarigha da Victor Boniface da kuma Gift Orban, yayin da aka kira Bruno Onyemaechi da kuma Raphael Onyedika.

Najeriya mai maki 12 da ke jan ragamar teburin farko bayan karawa biyar, tuni ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a buga a Ivory Coast cikin 2024.

Guinea Bissau ce ta biyu da maki 10, wadda za ta karɓi baƙuncin Saliyo.