Takarar Sanata: Hamayyar Dankwambo da Inuwa Yahaya ta dawo

Bayan shekaru ana fafatawa a siyasar Gombe, gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya da tsohon gwamna kuma Sanata, Ibrahim Hassan Dankwambo na shirin sake gwabza wa a takarar Sanatan Gombe ta Arewa maso Gabas gabanin zaɓen 2027. Dankwambo, wanda ya zama Gwamnan jihar daga 2011 zuwa 2019 kafin ya koma Majalisar Dattawa a 2023, na neman […]

Takarar Sanata: Hamayyar Dankwambo da Inuwa Yahaya ta dawo

created by photogrid

Bayan shekaru ana fafatawa a siyasar Gombe, gwamnan jihar Muhammad Inuwa Yahaya da tsohon gwamna kuma Sanata, Ibrahim Hassan Dankwambo na shirin sake gwabza wa a takarar Sanatan Gombe ta Arewa maso Gabas gabanin zaɓen 2027.

Dankwambo, wanda ya zama Gwamnan jihar daga 2011 zuwa 2019 kafin ya koma Majalisar Dattawa a 2023, na neman wa’adi na biyu, yayin da Inuwa Yahaya, da ke kammala wa’adinsa na biyu a matsayin Gwamna, shi ma ke neman kujerar.

A ƙarshen mako ne Inuwa Yahaya ya samu tikitin takarar Sanata na jam’iyyar APC, yayin da PDP ta amince da Dankwambo a matsayin ɗan takararta ta maslaha.

An gudanar da taron tabbatar da Dankwambo a ofishin PDP na yankin Gombe ta Arewa da ke Malam Sidi, inda shugabannin jam’iyya da masu ruwa da tsaki daga ƙananan hukumomi biyar suka halarta.

Hamayyar siyasar tsakanin Inuwa Yahaya da Dankwambo ta samo asali tun shekarar 2011 lokacin da Yahaya, wanda a wancan lokaci kwamishinan kuɗi ne a gwamnatin Danjuma Goje, ke neman zama gwamna.

Sai dai tsohon Gwamnan, Danjuma Goje ya marawa Dankwambo baya, lamarin da ya janyo takun-saƙa tsakanin ɓangarorin.

Masana siyasa na ganin fafatawar 2027 za ta kasance ɗaya daga cikin manyan gumurzu a siyasar Gombe, musamman ganin yadda duka ɓangarorin ke da magoya baya masu ƙarfi a jihar.