Tinubu ya sanya hannu kan N68.32trn a matsayin kasafin 2026, ya kara tsawaita wa’adin na 2025
Tinubu ya gode wa Majalisar Tarayya bisa amincewa da kasafin kuɗin cikin gaggawa.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026, wanda kai jimillar Naira tiriliyan 68.32.
Haka kuma ya amince da ƙara tsawaita wa’adin aiwatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 daga 31 ga watan Maris, 2026 zuwa 30 ga watan Yuni, 2026.
- Da gangan jiragen soji suka kai hari Kasuwar Jilli —Minista
- Katsina ta kafa kotunan tafi da gidan ka don gaggauta hukunta ’yan ta’adda
Kasafin kuɗin 2026 ya ƙunshi kuɗaɗen tafiyar da harkokin gwamnati, biyan basussuka, da kuma ayyukan ci gaba.
Babban ɓangare na kuɗin an ware shi ne domin ayyukan gina ƙasa kamar su ababen more rayuwa, wanda ke nuna ƙudirin gwamnati na bunƙasa tattalin arziƙi, tsaro, da inganta rayuwar al’umma.
Tsawaita wa’adin kasafin 2025 zai ba ma’aikatu da hukumomin gwamnati damar kammala ayyukan da ake yi da kuma amfani da kuɗaɗen da aka ware yadda ya kamata.
Shugaba Tinubu, ya umarci hukumomin gwamnati su riƙa amfani da kuɗin jama’a cikin kulawa da gaskiya, tare da tabbatar da kammala ayyuka a kan lokaci.
Ya kuma gode wa Majalisar Tarayya bisa gaggauta amincewa da kasafin, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziƙi, samar da ayyukan yi, da tallafa wa ’yan ƙasa.
Jan hankali: An yi amfani da wannan hoto ne domin buga misali.