Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci

Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna

Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci da aka yi a birnin Landan na Burtaniya.

A farkon makon nan ne dai Nafisa Abdullahi Aminu da Rukayya Muhammad Fema da kuma Hadiza Kashim Kalli suka zama zakaru a gasar TeenEagle ta 2025 da aka yi a birnin na Landan.

A cikin wata sanarwa daga bakin kakakinsa, Bayo Onanuga, ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce nasarar ’yan matan abin alfahari ce ga Najeriya.

Tinubu ya kuma yaba wa makarantun da daliban suke karatu, inda ya ce nasarar daliban wata alama ce ta kyau da ingancin karatun Najeriya da suke samar da hazikan dalibai da duniya ke alfahari da su.

Shugaban ya kuma yaba wa daliban tare da shawartar su da su ci gaba da mayar da hankali a kan karatunsu, sannan ya yi musu fatan nasara a rayuwa.