Ukraine ta roki UEFA kar ta dawo da Rasha cikin wasannin Turai
UEFA ta ce za a yi hakan ne bisa sharadin cewa babu kowanne wasa da zai gudana cikin Rasha.
Hukumar Kwallon Kafar Ukraine ta yi barazanar cewa za ta kaurace wa dukkanin wata gasa karkashin UEFA da aka bai wa Rasha damar komawa cikinta.
A ranar Talata ce UEFA ta sanar da cewa tawagar kwallon kafar Rasha ta ‘yan kasa da shekaru 17 za ta iya fafatawa a gasar nahiyar bayan dakatarwar watanni 19 da aka yi wa kasar tun bayan da ta kaddamar da mamaya kan Ukraine.
- ’Yan majalisa na barazanar tsige Shugaban Amurka Joe Biden
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Hukuncin Zaben Gwamnan Kaduna Ke Nufi
Sai dai a wata sanarwa da hukumar kwallon kafar Ukraine ta fitar ranar Laraba, ta ce ko shakka babu idan har UEFA ta amince da dawowar tawagar Rasha cikin wasannin nahiyar kai tsaye ita za ta fice daga ciki.
Sanarwar ta roki UEFA da kada ta amince da matakin dawowar tawagar ta Rasha cikin dukkanin gasar Turai.
Kwamitin zartaswar hukumar ta UEFA ne ya mika bukatar ganin an dawo da kasar ta Rasha cikin gasar ta cin kofin nahiyar Turai ta ‘yan kasa da shekaru 17 bisa sharadin cewa babu kowanne wasa da zai gudana cikin Rasha haka zalika babu dan wasan da zai sanya rigar Rasha ko kuma daga tutar kasar.
Wasan karshe na gasar zakarun Nahiyar ta Turai dai zai gudana ne a Cyprus badi haka zalika ta bangaren mata a Sweden cikin watan Mayu.