Wata mata da yara 2 sun tsere daga hannun ’yan ta’adda a Borno
Rundunar ta ce za ta ƙara ƙaimi wajen kai wa ‘yan ta’adda hare-hare.
Sojojin Operation Hadin Kai sun karɓi wata mata da yara biyu da suka tsere daga hannun ’yan ta’adda a dajin Sambisa da ke Jihar Borno.
Majiyoyin tsaro sun ce sojojin Bataliya ta 114 sun karɓe su a sansanin soji na Izge, da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza, a ranar 15 ga watan Yuni.
- Yadda aka sayar da jariri sabon haihuwa N2.5m a Legas — ’Yan Sanda
- Idan na ci zaɓe zan sasanta da ’yan bindigar da suka shirya ajiye makamai — Obi
Waɗanda aka ceto sun haɗa da Falmatu Ibrahim mai shekaru 30, Yabo Modu ɗan shekaru bakwai da kuma Sadiq Modu mai shekaru huɗu kacal a duniya.
Rahotanni sun nuna cewa sun tsere ne daga yankin Gazua da ke dajin Sambisa, inda suka yi tafiya har suka isa sansanin sojoji.
Falmatu ta shaida wa jami’an tsaro cewa hare-haren da sojoji ke kai wa ’yan ta’adda ne suka ba su damar tserewa.
Ta kuma bayyana cewa ita ’yar Ƙaramar Hukumar Konduga ce, kuma an yi garkuwa da ita a Dalori kusan shekara guda da ta gabata.
Bayan tantance su da yi musu rajista, an miƙa su ga rundunar soji ta 26 domin samun ƙarin kulawa da tallafi.
Hukumomin soji sun ce wannan nasara na nuna yadda hare-haren da ake ci gaba da kai wa ’yan ta’adda ke raunana su tare da bai wa waɗanda aka yi garkuwa da su damar samun ’yanci.
Sun ƙara da cewa duk da cewa tsaro ya inganta a yankin Arewa maso Gabas, sojoji na ci gaba da gudanar da ayyuka da nufin kawo ƙarshen ta’addanci gaba ɗaya.