Ya hallaka budurwarsa da wuƙa kan cacar-baki

Kwamishinan ya ce rundunar ta kama wani ɗan fashi da makami a jihar.

Ya hallaka budurwarsa da wuƙa kan cacar-baki

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Delta, ta cafke wani matashi Raphael Egb, ɗan shekara 20 kan zargin daɓa wa budurwarsa mai shekara 19, Jessica Uzowanne wuƙa, kan rashin jituwa da suka samu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Abaniwonda Olufemi ne, ya bayyana haka ga manema labarai a Asaba.

Ya kuma ce rundunar ta kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane, wanda ya yi wa wata fyaɗe.

Olufemi, ya bayyana cewa wanda ake zargin dan fashi ne da makami da ya addabi yankin Abraka da ke jihar wanda ya ce ya yi wa ɗaya daga cikin waɗanda suka yi fashi fyaɗe.

Kazalika, ya ce rundunar ta sake kama wani Nicholas Charles, wanda ake zargi da kashe wata Ngozi Sharon William.

“Yayin da Ngozi ta kai wa Nicholas ziyara, sai suka samu rashin jituwa tsakaninsu, hakan ya sa ya ɗauko wuƙa tare da daɓa wa matashiyar wanda ya yi sanadiyyar mutuwarta.”

A karon farko Tinubu zai tattauna da ’yan Najeriya kai-tsaye

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogara da wani yanki ba – Ndume