Yadda ake sayen kuri’u a Zaben Gwamnan Kogi
Wakilinmu ya ruwaito yadda jama’ar jihar ke tattauna yadda ake musu alkawairn N5,000 idan suka zabi dan takarar da aka yi musu tayi.

Daya daga cikin rumfunan zabe a Ekiti. An yi Allah-wadai da yadda ake sayen kuri’u
A yayin da ake gudanar da zaben gwamna a Jihar Kogi an samu rahotannin sayen kuri’u a wasu rumufuna.
Wakilinmu ya ruwaito yadda jama’ar jihar ke tattauna yadda ake musu alkawairn N5,000 idan suka zabi dan takarar da aka yi musu tayi.
- ’Yan daba sun bude wa masu zabe wuta a Bayelsa
- Hisbah ta cafke mutum 37 kan karuwanci da sayar da giya a Yobe
Wakilinmu ya samu mutane na tattauna wannan batu a rumfar zabe da ke Miami daura da Adankolo a garin Lokoja inda ya ga wakilin wata jam’iyya na sanya ido domin tabbatar da jam’iyyar da masu zabe suka dangwala wa kafin biyan su.
Irin haka na faruwa a Angwa Pawa da ke garin na Lokoja, inda ake kiran musamman mata gefe a ba su kudi, wasu tun kafin ma su yi zabe.