Yadda Boko Haram ta kashe jami’an tsaro 37 a Yobe

Wani jami’in sa-kai ya shaida wa wakilinmu cewa sama da sojoji 20 ma sun mutu a harin

Yadda Boko Haram ta kashe jami’an tsaro 37 a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ya tabbatar da kashe jami’anta 17 tare da wasu sojoji a wani hari da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram suka kai makarantar horas da rundunar musamman ta sojoji da ke Buni Yadi a Ƙaramar Hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

Wani jami’in sa-kai ya shaida wa wakilinmu cewa sama da sojoji 20 ma sun mutu a harin, duk da cewa rundunar sojin Najeriya ba ta bayyana adadin jami’an da ta rasa ba.

Ya ƙara da cewa an kwashe gawarwakin jami’an tsaron zuwa Asibitin Koyarwa na Damaturu kafin daga baya aka tura su Maiduguri domin jana’iza.

Kakakin rundunar ’yan sanda, Anthony Okon Placid, ya ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:15 na dare a ranar 8 ga watan Mayu, 2026.

Ya bayyana cewa jami’an ’yan sandan na cikin wani horo na musamman kan dabarun yaƙi da ta’addanci ne lokacin da maharan suka kai farmaki daga wurare daban-daban.

A cewarsa, jami’an sun rasa rayukansu ne yayin kare ƙasa daga harin ’yan ta’addan.

Rahotanni daga Buni Yadi sun ce an shafe sama da sa’o’i uku ana musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da maharan kafin ’yan ta’addan suka janye.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya ce jami’an da suka mutu sun mutu a matsayin jarumai masu kishin ƙasa, yana mai cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da farautar wadanda suka kai harin.