Yadda jami’an tsaro suka kashe ’yan ta’adda a musayar wuta 50 a Neja
’Yan ta’addar saboda tsabar girgiza, sun riƙa sassara gawarwakin abokansu suna sanyawa a cikin buhuna, suna tafiya da su
Jami’an tsaro sun halaka aƙalla ’yan ta’adda 50 a yayin wata musayar wuta a yankin Ƙaramar Hukumar Mariga da ke Jihar Neja.
Haɗin gwiwar sojoji da sauran tsaro ne suka aika ’yan ta’addan lahira ne a yayin wata ƙazamar arangama a yankin Kumbashi da ke Ƙaramar Hukumar.
Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Neja, muka wakilin Ƙaramar Hukumar Mariga a majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun yi nasarar kuɓutar da wasu mutane da ’yan ta’addan suka yi garkuwa da su.
Abdulmalik Sarkin-Daji, ya sanar da haka ne a garin Kontagora, yana mai jinjina wa jami’an tsaro.
- Gwamnonin Arewa maso gabas za su yi taro kan matsalar tsaro
- Harbe soja: ’Yan sanda da Sojoji na binciken dalili a Bauchi
Ya ruwaito shaidu na cewa ’yan ta’adda kimanin 300 ɗauke da makamai ne suka yi yunƙurin kutsawa ƙauyen a ranar Talata.
“Sun yi nufin kai hari ne a wani sansanin Hukumar Tsaro ta DSS, amma jami’an tsaron suka mayar da martani suka kashe kimanin 50 daga cikin ’yan bindigar, wasu da dama kuma suka tsere ɗauke da raunukan harbi.
“Al’ummar mazaɓata sun tabbatar min cewa sun ga yadda ’yan ta’addar, saboda tsabar girgiza, suka riƙa sassara gawarwakin abokansu suna sanyawa a cikin buhuna, suna tafiya da su a kan baburansu.”
A wani labari makamancin wannan kuma, ’yan bindiga sun kashe wani manomi tare da jikkata wasu a yankin Kundu da ke kusa da garin Zungeru a Ƙaramar Hukumar Rafi a ranar Alhamis.