Yadda na taso daga almajiranci na zama shugaban NNPCL – Kyari
Kyari, ya bayyana irin wahalhalun da ya fuskanta a rayuwa.
Shugaban Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya bayyana yadda ya taso a matsayin almajiri har ya zama shugaban kamfanin makamashi mafi girma a Afrika.
A yayin da yake bikin cika shekaru 60 a duniya, Kyari ya yi wa Allah gidiya bisa nasarorin da ya samu a rayuwa.
- Shugaban ’yan sandan Mopol na Legas ya Musulunta a Kano
- Sojoji da dama sun ɓace bayan harin Boko Haram a Borno
“Ina matuƙar godiya ga ƙasata da ta ba ni dama daga almajiranci har na zama shugaban babban kamfanin makamashi a Afrika,” in ji Kyari.
“Ina gode wa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa damar da suka ba ni na zama shugaban ƙarshe a NNPC da kuma shugaban farko na NNPCL.”
Kyari, ya bayyana ƙalubale da nasarorin da ya fuskanta a rayuwarsa, inda ya danganta su da ikon Allah.
Ya ce, “Tunani kawai ba zai iya bayyana yadda rayuwata ta kasance ba—na sha wahala, na ji daɗi, raɗaɗi da farin ciki, gazawa da nasarori. Allah ne kaɗai zai iya bayyana wannan.”
Ya kuma gode wa iyalansa, abokansa, da abokan aikinsa bisa goyon bayan da suka ba shi.
Ya jaddada cewa hakan zai ƙara masa ƙwarin gwiwa don ci gaba da yi wa ƙasarsa aiki.