Yadda sojoji suka kashe ’yan ta’adda 817, suka ceto mutum 720 a wata 3
Sojoji sun kwato makamai 3,269, bayan sun cafke mutum 1,326
Hedikwatar Tsaron Najeriya ta ce sojoji sun kashe ’yan ta’adda 817, suka ceto mutum 721 daga hannun ’yan bindiga a wata uku da suka gabata a kasar.
Sojoji sun kuma kwato makamai bindigogi da albarusai 3,269, bayan sun cafke mutum 1,326 masu manyan laifuka, ciki har da ’yan Boko Haram, ’yan bindiga, masu musu leken asiri, ’yan IPOB, ’yan fashi da kuma dillalan makamai.
- Ruftawar kasa ta kashe mutum 30, an sace wasu 19 a Abuja
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Bambanta Sheikh Giro Argungu Da Sauran Malamai
Kakakin hedikwatar tsaro, Manjo-Janar Edward Buba ya ce sauran sun hada da barayin shanu, barayin danyen maida kuma barayin karfen titin jirgin kasa.
Janar Edward Buba ya shaida wa taron ’yan jarida a Abuja cewa, mayakan Boko Harma da ISWAP tare da iyalansu mutum 4,560 sun mika wuya ga sojoji a yankin Arewa maso Gabas a cikin watanni ukun.
Sojoji sun kama ’yan Boko Haram da ISWAP, 240, da masu taimaka musu guda 276, suka kuma ceto mutum 147 da kungiyoyin suka yi garkuwa da su.
Ya ce abuwan da aka kwato sun hada da dabbobi 3,577, da sauran wasu abubuwa guda 674.
A tsawon watanni ukun a yankin Arewa maso Gabas, sojoji sun kwato bindigogi 169 ciki har da guda 57 kirar AK47, da kuma albarusai 1,195 da gurneti guda uku.
A Arewa ta Tsakiya, sojoji sun aika ’yan ta’adda 83 lahira, sun cafke wasu 104, suka ceto mutane 18 da aka yi garkuwa da su, sannan suka kwato bindigogi 37 da harsasai 68 da sauran kayan laifi.
A yankin Arewa maso Gabas kuma sojoji sun kashe ’yan ta’addan 248, sun cafke 116, suka ceto musu 359 da aka yi gakruwa da su sannan kwato bindigogi 67, albarusai 926 da sauran wasu kayan laifi 160.
A Kudu maso Kudu an kashe mayakan sa-kai 69 fighters, an kama barain danen mai 191 sananan aka ceo muum 12 da aka i garkuwa da su.
An kama lita miliyan 6.6 da danyen man sata, da lita miliyan 3.5 na haramtaccen gas da kananzir lita miliyan 1.8 da kuma fetur lita 65,600.
Sojojin sun kuma kama tare da lalata jiragen ruwa uku da kananan jiragen ruwa 249 da injinan ban-ruwa 28 suka kwato bindigogi 51.
Kakakin sojojin ya ce dakarun sun kuma kashe mayakan sa-kai O80 a yankin Kudu maso Gabas, ya cafke ‘yan IPOB 162 IPOB/ESN suka ceto mutum 109 daga hannun masu garkuwa da mutane.
Sun kwato bindigogi 63, harsasai 320 da sauran kayan laifi guda 166.