’Yan bindiga sun hallaka mutum 46 a Neja
Harin ya fi muni a ƙauyen Konkoso, inda aka kashe aƙalla mutum 38 ta hanyar harbi ko kuma yankan rago.
’Yan bindiga sun hallaka aƙalla mutane 46 a wasu hare-hare da suka kai wasu ƙauyuka a Jihar Neja, inda suka yi wa wasu daga cikin waɗanda harin ya shafa yankan rago.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa lamarin ya faru a ranar Asabar, inda ’yan bindigar suka far wa garuruwa uku, cikinsu har da Tungan Makeri da Pissa da ke Karamar Hukumar Borgu, mai iyaka da Jihar Kwara.
- Yadda gobara ta sake tashi a kasuwar Singa
- Za mu kawo wa Tinubu da Abba ƙuri’u masu yawan gaske a 2027 — Barau
Wata majiyar tsaro ta ce ’yan bindigar sun kai harin ne a kan aƙalla babura 41, kuma kowanne yana ɗauke da mutum biyu ko uku.
Bayanai sun ce harin ya fi muni a ƙauyen Konkoso, inda aka kashe aƙalla mutum 38 ta hanyar harbi ko kuma yankan rago.
Ana kuma fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu a hare-haren zai iya zarta hakan, la’akari da cewa ’yan bindigar sun ƙone gidaje da dama da ba a san adadi ba.
Ko a farkon wannan wata na Fabarairu mahara sun kashe mutane sama da 160 a Jihar Kwara, wadda ita ma ke shiga cikin jerin jihohin arewacin Najeriya masu fama da tashe-tashen hankula daga ’yan ta’adda.
Sauran jihohin sun haɗa da Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Sakkwato.