’Yan bindiga sun harbe dan sanda har lahira a Zamfara

Maharan sun yi wa ‘yan sandan ƙawanya tare da bude musu wuta.

’Yan bindiga sun harbe dan sanda har lahira a Zamfara

Wasu ‘Yan Bindiga sun kai hari shingen binciken ’yan sanda da ke kauyen Tazame a Jihar Zamfara, inda suka harbe dan sanda daya har lahira tare da raunata wasu.

Shingen na da nisan kilomita daya zuwa garin Kwatarkwashi, wanda ke kusa da Gusau, babban birnin jihar.

Majiyoyi da dama sun shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sama da 40, tare da bude wa shingen wuta da misalin karfe 4 na safiyar ranar Lahadi.

Majiyar ta ce maharan sun kuma banka wa shingen wuta tare da kone komai kafin daga bisani suka tsere zuwa daji.

“’Yan bindigar sun yi wa ’yan sandan da ke wurin yawa inda suka dinga musayar wuta na tsawon lokaci.

“Na samu labarin cewa sauran ’yan sandan sun tsere domin ceton rayukansu. Maharan sun fi ‘yan sanda yawa. An yi sa’a wasu daga cikin ‘yan sandan sun tsere da dukkaninsu za su hallaka.”

Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, domin jin ta bakinsa, ya ci tura, domin bai amsa kiran da aka masa ba.

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin Arewa da ke ci gaba da fuskantar kazaman hare-haren ta’addancin ’yan bindiga.

Gobarar tankar mai ta yi ajalin mutum 18 a Enugu

An yi taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin harin ’yan ta’adda a Kano

An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila

Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania