’Yan bindiga sun sa wa manoma harajin N10m a Katsina

’Yan bindiga sun sace mata da kananan yara 15 tare da kakaba wa manoma harajin Naira miliyan 10 a Jihar Katsina

’Yan bindiga sun sa wa manoma harajin N10m a Katsina

’Yan bindiga sun sace akalla mutum 15, galibinsu mata, yara da jarirai, a Karamar Hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

A wani rahoton kuma, ’yan bindiga sun kakaba harajin Naira miliyan 10 ga wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Faskari da Bakori.

An ce wannan haraji sharadi ne domin manoma su samu damar shiga gonakinsu a lokacin damina ba tare da fargaba ba.

Aminiya ta ruwaito cewa harin Karamar Hukumar Bakoti ya faru ne a ƙauyen Sabon Layi da ke gundumar Kakumi da misalin ƙarfe 9:45 na dare a ranar Alhamis,.

Wata majiya ta ce maharan sun yi aiki cikin tsari, inda suka rabu gida biyu; wani bangare suka yaudari jama’a da satar shanu, yayin da dayan bangaren suka shiga cikin ƙauyen suka sace mutane.

An ce maharan sun tsere ba tare da sun yi harbi ba, domin kauce wa jawo hankalin jama’a.

An kuma bayyana cewa sun bi ta wata hanya da aka saba amfani da ita wajen tserewa zuwa wani yanki na kusa.

Duk kokarin da jami’an tsaro na al’umma da ’yan sintiri suka yi na bin sawun maharan ba a yi nasara ba, domin sun riga sun tsere.

A cikin wadanda aka sace akwai yara kanana da jarirai, lamarin da ya kara tayar da hankalin al’umma.