’Yan bindiga sun kashe mutum 5, sun jikkata 2 a Kaduna

Mazauna yankin sun nemi hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa kan hare-haren.

’Yan bindiga sun kashe mutum 5, sun jikkata 2 a Kaduna

Aƙalla mutum biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon wani hari da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai a daren ranar Laraba a garin Gidan Waya da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna.

Lamarin ya faru ne lokacin da maharan suka shiga yankin da daddare tare da buɗe wa mazauna garin wuta.

Wani mazaunin garin da ya zanta da Aminiya, da safiyar ranar Alhamis ya bayyana cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da mafarauta hudu da kuma wani mutum guda ɗaya.

Majiyar, wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta ce maharan sun isa ne da misalin ƙarfe 9 na dare, inda suka nufi ofishin ’yan sintiri na mafarauta tare da fara harbi ba kakkautawa.

“Mun fara jin karar harbe-harbe da misalin ƙarfe 9 na dare, nan da nan mutane suka fara gudu domin tsira da rayukansu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa bayan harin ya lafa, mazauna yankin tare da Hakimin Gidan Waya sun isa wajen domin kwashe waɗanda abin ya shafa.

“Mutane huɗu daga cikin waɗanda aka kashe mambobi ne na ƙungiyar mafarauta da wani mutum. Daga baya muka kai waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Anglican da ke Gidan Waya inda ake kula da su,” in ji shi.

Wani mazaunin gari, ya kuma tabbatar da cewa an yi jana’izar wasu daga cikin waɗanda suka mutu bisa koyarwar addinin Musulunci.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, domin tabbatar da faruwar lamarin bai yi nasara ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Mazauna yankin sun bayyana damuwa kan harin tare da kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakai domin dawo da zaman lafiya a yankin.