’Yan bindiga sun kashe ’yan sa-kai 2 a Filato

Al’ummar yankin sun koka kan yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

’Yan bindiga sun kashe ’yan sa-kai 2 a Filato

’Yan bindiga sun kashe wasu ’yan sa-kai biyu a ƙauyen Ta-Hoss da ke Ƙaramar Hukumar Riyom ta Jihar Filato.

Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Laraba lokacin da mutanen biyu ke sintiri domin kare al’ummarsu.

Mutanen da suka kashe haɗa da Davou Dalyop Patu mai shekara 48 da Dalyop Zaram mai shekara 38.

Dukkaninsu mambobi ne na ƙungiyar masu ’yan sa-kai da ke taimakawa wajen kare al’umma daga hare-hare.

Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali, yayin da jama’a ke nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke ci gaba da addabar ƙauyukan Ƙaramar Hukumar Riyom.

Wani jagoran al’umma, Livinus Badung, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana mamatan a matsayin jajirtattun mutane waɗanda suka sadaukar da kansu wajen tabbatar da tsaron al’ummarsu.

Ya ce mutuwarsu ta girgiza tare da sanya al’ummar yankin cikin baƙin ciki.

Shi ma Rwang Tengwong, Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Matasan Berom (BYM), ya nuna alhininsa kan kisan, tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da al’ummar Ta-Hoss.

Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da kamo waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Oteh, bai mayar da martani kan tambayoyin da aka yi masa dangane da lamarin ba.