HOTUNA: Hausawa sun yi zanga-zanga a Ibadan kan danganta su da satar mutane
Hausawan sun koka kan yadda ake tsangwamarsu saboda laifukan da wasu tsiraru suka aikata.
Wasu daga cikin al’ummar Hausawa mazauna Ibadan, babban birnin Jihar Oyo, sun gudanar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu kan alaƙanta su da laifukan satar mutane da ke faruwa a jihar.
Masu zanga-zangar sun ce ba daidai ba ne a riƙa danganta dukkanin Hausawa da aikata laifuka saboda laifin wasu tsiraru.
- An kama mutum 2 sun yi wa wata mata fashi a Abuja
- NAJERIYA A YAU: Yadda Masu Yi Wa Kasa Hidima Za Su Ci Arzikin Yankunan Da Suke AIki
Wannan zanga-zanga na zuwa ne makonni kaɗan bayan sace ɗalibai da malamai 46 a wani hari da aka kai makarantu uku a Ƙaramar Hukumar Oriire a jihar.
Al’ummar Hausawan sun buƙaci jama’a da hukumomi su guji yi musu kallon masu laifi saboda asalinsu ko ƙabilarsu, tare da jaddada cewa mafi yawan Hausawa mazauna jihar mutane ne masu zaman lafiya da bin doka.
Ga wasu daga cikin hotunan zanga-zangar: