’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda da mutanen gari a Zamfara

‘Yan sanda sun yi artabu da maharan inda su ma suka yi nasarar kashe 11 daga cikinsu.

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda da mutanen gari a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe mutum biyar, ciki har da jami’an ’yan sanda biyu da mutanen gari uku, a wani hari da suka kai wa al’ummar Yarkatsinan Laka da ke Ƙaramar Hukumar Bungudu a Jihar Zamfara.

Rundunar ’yan sandan Jihar Zamfara, ta ce maharan sun zo ne a kan babura sama da 50, ɗauke da makamai.

Jami’an ’yan sanda sun kai ɗauki cikin gaggawa, inda suka fafata da ’yan bindigar.

A yayin artabun, an kashe ’yan bindiga 11, yayin da wasu suka tsere da raunukan harbi.

Sai dai jami’an ’yan sanda biyu da wasu mutum uku sun rasa rayukansu.

Haka kuma wani jami’in ɗan sanda ya ji rauni, tuni aka garzaya da shi asibiti inda yake samun kulawar likitoci.

’Yan sanda sun ce zaman lafiya ya daidai a yankin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ahmad Muhammad Bello, ya ziyarci al’ummar yankin domin jajanta musu game da lamarin.

Ya kuma yi alƙawarin cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta tsaro da dawo da zaman lafiya.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin taimakawa wajen yaƙi da laifuka.