’Yan bindiga sun sace Basarake a Katsina
An yi awon gaba da su ne da wasu mata biyu gami da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance yawan su ba.
’Yan bindigar daji sun kai hari a ƙauyen Kogari da ke cikin ƙaramar hukumar Matazu ta Jihar Katsina inda suka yi awon gaba da Maigari na Kogari Alhaji Bello Abdulkarim tare da ɗiyarsa.
An yi awon gaba da su ne da wasu mata biyu gami da wasu mutanen da har yanzu ba a tantance yawan su ba, an kai harin ne a daren Talatar.
- Kwamishinan El-Rufai ya shiga takarar Gwamna a Jam’iyyar ADC
- Putin ya sauya gwamnonin jihohin Rasha biyu da ke iyaka da Ukraine
Kazalika, maharan sun yi awon gaba da matar wakilin Maigarin shi ma tare da ɗiyar shi.
Harin da shaidu da ido suka ce ya jefa jama’a cikin tararrabi a ƙaramar hukumar Matazu na daga cikin ƙananan hukumomin da ake zargin ƙasurgumin ɗan ta’addan nan mai suna Muhammadu Fulani ya addaba.
Shi dai Fulani shi ne wanda ya yi watsi da sasancin da aka yi da a su a kwanakin. Har zuwa haɗa wannan rahoto babu wata hukumar tsaro da tace uffan a kai