’Yan daba sun kai hari Kasuwar Waya ta Farm Center da ke Kano
Maharan sun shiga kasuwar ɗauke da makamai masu haɗari, suna kwashe kayayyaki a tsakar rana.
Kasuwar Wayoyi ta Farm Centre da ke Kano
Ana fargabar cewa wasu ’yan daba sun kai hari a wani sashe na Kasuwar Waya ta Farm Center da ke Kano, inda suka sace wayoyi da sauran kayayyaki na ’yan kasuwa da kwastomomi.
Rahotanni sun ce harin ya faru da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin ɗin nan, inda maharan suka shigo kasuwar ɗauke da makamai masu haɗari, suna kwashe kayayyaki a tsakar rana.
- An shiga tsaka mai wuya bayan ’yan tawaye sun kashe Ministan Tsaro a Mali
- Mun amince da tazarcen Tinubu da Namadi a 2027 — Dattawan APC a Jigawa
Wani ɗan kasuwa, Sanusi Almanzawy, ya ce lamarin ya tilasta rufe Yayo Plaza gaba ɗaya, yana mai cewa shagunan da ke ƙasa ne suka fi fuskantar ɓarna da satar wayoyi.
Haka kuma, wani ɗan kasuwa, Muhammad Aminu, ya ce maharan sun tare titin Zariya da ke daura da kasuwar na wani lokaci, lamarin da ya haddasa cunkoson ababen hawa.
’Yan kasuwar sun yi zargin cewa ’yan dabar sun kawo harin ne bayan wani taron siyasa da aka gudanar kusa da kasuwar, sai dai ba a tabbatar da hakan ba a hukumance.
Daga bisani jami’an ’yan sanda sun isa wurin, inda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa maharan.
Sai dai haƙar Aminiya ba ta cimma ruwa ba a yayin da ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar gabanin haɗa wannan rahoto.