’Yan majalisa na barazanar tsige Shugaban Amurka Joe Biden
Fadar White House ta ce binciken wani abu na neman son-a-sani na siyasa.
’Yan Majalisar Wakilan Amurka na jam’iyyar Republican sun soma yi wa Shugaba Joe Biden barazanar tsige shi daga kujerar mulki.
Lamarin dai na zuwa ne yayin da ’yan majalisar suka bayyana ranarsu ta farko ta kaddamar da bincike kan Shugaba Biden a matsayin nasara.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Hukuncin Zaben Gwamnan Kaduna Ke Nufi
- Dangin matar da suka ce an cire wa sassan jiki a asibitin Gombe sun lashe amansu
Sai dai biyu daga cikin ƙwararrunsu masu bayar da sheda sun ce zuwa yanzu babu isasshiyar shaidar da za ta tallafa wajen tsigewar.
Harkokin kasuwanci na ɗan shugaban ƙasar Hunter Biden su ne suka mamaye zaman da majalisar ta yi a ranar Alhamis na tattauna batun shirin tsigewar.
’Yan majalisar na jam’iyyar Republican sun yi zargin cewa Shugaba Biden ya amfana da harkokin kasuwancin dan nasa.
Sai dai a martanin da Fadar White House ta yi, ta bayyana binciken a matsayin wani abu na neman son-a-sani na siyasa.
’Yan majalisar na Republican sun yi shekaru suna gudanar da bincike a kan ɗan shugaban kamar yadda Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ita ma take yi.
Sai dai babu ɗaya daga cikinsu da ya samu shaidar da ke nuna cewa Joe Biden walau a matsayinsa na shugaban ƙasa ko mataimakin shugaban ƙasa ya saba wa ƙa’idojin aikinsa ko kuma ya karɓi cin hanci.