’Yan majalisa sun nemi Tinubu ya magance matsalar tsaro ko ya sauka daga kan mulki
Tsagin ‘yan adawar ya koka kan yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda a wasu sassan ƙasar nan.
’Yan Majalisar Wakilai tsagin ’yan adawa, sun nemi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya dakatar da harkokin siyasar zaɓen 2027 tare da mayar da hankali kan matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da suka addabi ƙasar nan.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Fred Agbedi, ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli masu tarin yawa da suka haɗa da garkuwa da mutane, kashe-kashe, talauci da tsadar rayuwa.
- ’Yan bindiga sun harbe hakimi har lahira a Filato
- Yadda aka sayar da jariri sabon haihuwa N2.5m a Legas — ’Yan Sanda
Ya zargi gwamnati da fifita siyasa a kan gudanar da mulki.
’Yan majalisar sun kafa misali da sace ɗalibai a jihohin Borno, Oyo da Kogi, tare da mutuwar tsohon Kakakin Hedikwatar Tsaro Manjo Janar Abubakar Rabe, a hannun ’yan bindiga.
Sun ce idan har tsohon babban jami’in soja ba shi da tsaro, to talakawan ƙasa za su fi kowa kasancewa cikin hatsari.
Tsagin ’yan adawar ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya dakatar da duk wani shiri na sake tsayawa takara a 2027, ya kuma ƙaddamar da shiri na watanni shida don inganta da tsaro da tattalin arziƙi.
Haka kuma sun nemi a ɗauki matakan gaggawa domin ceto ɗaliban da aka sace, bincike kan musababbin mutuwar Janar Rabe da kuma sake fasalin tsarin tsaron ƙasar.
Hakazalika, sun soki hukuncin kotu da ya umarci soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa guda biyar.
A cewarsu, wannan mataki na iya jefa jam’iyyun adawa cikin matsala gabanin zaɓen 2027, don haka suka buƙaci kotuna da INEC da su kare tsarin dimokuraɗiyya.
Game da tattalin arziƙi kuwa, sun buga misali da yadda ’yan Najeriya ke fama da yunwa, tsadar rayuwa, rashin tsaro da kuma faɗuwar darajar Naira.
Sun zargi jam’iyya mai mulki da mayar da hankali kan siyasar 2027 maimakon magance matsalolin da jama’a ke fuskanta.
Dangiwa Umar ya nemi Tinubu ya bai wa tsaro muhimmanci
Tsohon gwamnan mulkin soja na Jihar Kaduna, Abubakar Dangiwa Umar, shi ma ya buƙaci shugaban ƙasa da ya mayar da hankali kan tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.
A wata wasiƙa da ya aike wa shugaban, ya ce kare rayukan jama’a shi ne babban nauyin da ke kan kowace gwamnati.
Ya ƙara da cewa babu wani ci gaba ko dimokuraɗiyya da za su yi tasiri idan babu tsaro.
An kashe mutum 390, an sace 202 a watan Mayu — NHRC
Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Ƙasa (NHRC), ta bayyana cewa an kashe mutum 390 tare da sace wasu 202 a faɗin Najeriya a watan Mayun 2026.
Hukumar ta ce kai wa makarantu, wuraren ibada da fararen hula hare-hare na ci gaba da ƙaruwa, lamarin da ke nuna yadda matsalar tsaro ke ƙara ta’azzara a ƙasar.
Gwamnati ta ce tana ɗaukar natakan daƙile rashin tsaro
A nata ɓangaren, Gwamnatin Tarayya ta ce tana ƙoƙarin kawo ƙarshen ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane.
A jawabinsa na ranar Ɗimokuradiyya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce gwamnati na shirin ɗaukar sabbin ’yan sanda sama da 50,000 tare da ware maƙudan kuɗaɗe domin harkokin tsaro a kasafin kuɗin 2026.
Ya kuma ce jami’an tsaro sun kashe dubban ’yan ta’adda a cikin shekarar da ta gabata, yayin da wasu da dama suka ajiye makamansu a ƙarƙashin shirin sulhu na gwamnati.
Tinubu ya gargaɗi masu garkuwa da mutane, ’yan bindiga da masu ɗaukar nauyin ta’addanci da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci ƙarfin gwamnati, yana mai jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Najeriya.