’Yan sanda sun cafke jami’in DSS na bogi a Jigawa
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta cafke wani matashi dan shekara 27 da ke yin sojan gona a matsayin jami’in tsaro na DSS
’Yan sanda A jihar Jigawa sun cafke wani matashi dan shekara 27 da ke yin sojan gona a matsayin jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shi’isu ya ce dubun jami’an DSS na bogin ta cika ne bayan da ya damfari wasu daliban Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Jigawa da cewa zai sama musu aikin DSS da kuma hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
- Kotu ta kori bukatar INEC, NNPP da Abba na korar karar APC
- Kotu ta kori karar APC kan haramcin takarar Abba
DSP Shi’isu ya bayyana cewa wanda ake zargin ya karbi kudin da yawansu ya kai Naira 305,000 da cewa zai sama musu aikin DSS da NDLEA.
Ya ce a ranar 16 ga watan Agusta dubun dan damfarar ta cika, ya fada komar rundunar bayan ta samun rahoto, inda jami’anta da ke dutse suka shiga farautar sa, inda suka kama shi da wandon kakin DSS.
Shi’isu ya ce rundunar ta kuma cafke wani dan shekara 26 kan zargin fashi da makami a Karamar Hukumar Gwaram, wanad aka kama shi da wata karamar bindiga kirar gida.
Ya ce a wanda ake zargin ya shaida musu cewa ya sayo bindigar ne daga Jihar Nasarawa, inda suke kwacen babura.
Rundunar ta kuma cafe wasu mutum biyu masu shekara 20 kowannensu da suka shiga wani gida suka saci tufa da kayan kallo da sauran kayan amfani da kimarsu ta kai Naira miliyan 3.5.
Bayan samun rahoto daga al’umma, rundunar ta kuma cafke wani wanda ke sace fitilun kan titi a wata unguwar masu kudi a garin Dutse.
Ya ce dukkansu za a gurfanar da su a kotu da zarar rundunar ta kammala bincike.