’Yan sanda sun kashe ’yan IPOB 5 a Ebonyi
Sai dai jami’an ofishin sun ci karfinsu a wani artabu na tsawon mintuna 30, inda a aka kona motocin ’yan sanda a yayin musayar wuta.
Akalla ’yan kungiyar IPOB biyar aka kashe a wani artabu da ’yan sanda a Jihar Ebonyi ranar Laraba.
’Yan kungiyar a cikin wata motar bas sun kai hari da misalin karfe 9:30 na dare a ofishin ’yan sanda da ke Ishieke a Karamar Hukumar Ebonyi inda suka bude wuta.
Sai dai jami’an ofishin sun ci karfinsu a wani artabu na tsawon mintuna 30, inda a aka kona motocin ’yan sanda a yayin musayar wuta.
Aminiya ta gano cewa jami’ai daga hedikwatar ’yan sandan jihar da sojoji ne suka kai dauki bayan samun kiran gaggawa daga ofishin ’yan sandan na Ishieke.
- Aminu Ado Bayero ya daga tuta a Fadar Nassarawa
- NAJERIYA A YAU: Kimar Sarakunan Gargajiya A Idon Al’ummar Arewa
Wata majiya mai tushe ta ce karar harbe-harben ya tilasta wa mazauna garin guduwa domin tsira da rayukansu.
Majiyar ta ce maharan sun yi kokarin su tsere, amma suka gamu da ajalinsu a hanya a hannun jami’an tsaron.
Rundunar ’yan sandan ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
Amma shaidu sun ce a kai motar da ’yan IPBOB din suka yi amfani da ita da kuma gawarwakinsu hedikwatar ’yan sandan jihar.