’Yan ta’adda sun kai wa sojoji hari a Edo

daya daga cikin sojojin yana cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, sauran biyu kuma samu munanan raunuka.

’Yan ta’adda sun kai wa sojoji hari a Edo

Wasu sojoji Uku sun tsallake rijiya da baya a wani hari da ’yan bindiga suka kai musu a Jihar Edo.

Gwamnatin jihar ta sanar cewa ’yan bindiga sun kai wa sojojin hari ne a wani kamfanin manja da sojojin suke fadi a Karamar Hukumar Ovia ta Kudu maso Yamma a jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Chris Nehikhare, ya ce daya daga cikin sojojin yana halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, sauran biyu kuma samu munanan raunuka.

Ya sanar a lokacin da ya je dubiyar sojojin a asibiti ya ce an kai musu hari ne a kamfanin manja na Okomu Oil a ranar Juma’a.

A cewarsa, hukumomin jihar na yin abin da ya kamata domin kawar da duk ’yan ta’adda da ke shiga rigar kungiyoyin asiri da dangoginsu.

Nehikhare ya kara da cewa an kafa rundunar aiki da cikawa ta musamman domin wannan aiki karkashin jagorancin Daraktan hukumar naD DSS.

A cewar kwamishinan, Gwamna Godwin Obaseki ya yi alkawarin biyan kudi jinyar sojojin da kuma daukar matakan da za su zama darasi kan duk masu kunnen kashi da ke kai irin wadannan hare-hare a jihar.

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Tags