’Yan ta’adda sun kashe sojoji 7 a Sakkwato

Bayanai sun ce mayaƙan Lakurawa sun kai wa dakarun farmaki ne a yayin da suke ƙoƙarin gyara motar su da ta lalace a kan hanya.

’Yan ta’adda sun kashe sojoji 7 a Sakkwato

Aƙalla sojojin Najeriya bakwai ne suka rasa rayukansu a wani harin kwanton ɓauna da ake zargin mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kai musu a Jihar Sakkwato Arewa maso Yamma.

Majiyoyin soji da na cikin gida sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Asabar, lokacin da dakarun ke dawowa daga wani samame da suka kan sansanin ’yan ƙungiyar Lakurawa a garin Illela da ke iyakar Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.

Rahotanni sun ce mayaƙan sun kai wa sojojin hari ne bayan ɗaya daga ayarin motocinsu ta lalace a kan hanya, lamarin da ya tilasta mata tsayawa yayin da sauran motoci biyun suka ci gaba da tafiya.

Wata majiya ta shaida cewa mayaƙan Lakurawa sun kai wa dakarun farmaki ne a yayin da suke ƙoƙarin gyara motar, inda suka kashe sojoji bakwai ciki har da wani mai muƙamin Laftanar.

Wani mazaunin yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa soja guda ɗaya ne ya tsira daga harin, yayin da sauran suka rasa rayukansu.

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da faruwar harin, sai dai ba ta bayyana adadin waɗanda suka mutu ba.

Kakakin rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce an tura ƙarin dakarun gaggawa zuwa yankin domin ci gaba da kai farmaki da kuma fatattakar maharan.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro domin gano tare da murƙushe waɗanda suka kai harin.

Ƙungiyar Lakurawa, wacce ake alaƙanta ta da wasu ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel, ta ƙara ƙarfi a jihohin Kebbi da Sakkwato tun daga 2018, inda ta fara zama barazanar tsaro musamman daga shekarar 2023.

A baya, rahotanni sun nuna cewa an sha gudanar da hare-haren haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da ƙasashen waje kan sansanonin ƙungiyar a yankin.